Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce a kowacce shekara a na samun mutane dubu 15 zuwa dubu 20 waɗanda maciji ya ke cizo a fadin ƙasar.

Ƙaramin ministan lafiya a Najeriya Dakta Adeleke Mamora ne ya bayyana haka yayin taron da hukumar ta shirya don wayar da kai a dangane da cizon maciji.
Ministan ya ce akwai wasu da ake samu macijin ya cije su amma ba sa kai rahoton wajen jami’an lafiya.

Dankata mamora ya ce a na samun mutuwar mutane aƙalla dubu biyu a sanadin cizon maciji.

Ya ƙara da cewar an fi samun cizon macijin a jihohin Oyo, Adamawa, Benue, Plateau, Taraba, Kebbi, Norno, Bauchi, Nassarawa da jihar Enugu.
Minsitan ya buƙaci al’umar jihohin da su kasance masu kula tare da hada kai da kwamitin da ke yaƙi da cizon maciji don rage afkuwar hakan a nan gaba.
An gudanar da taron ne a Abuja ranar Litin domin tunawa da ranar yaƙi da cizon maciji ta duniya.