Rundunar ƴan sandan Najeriya sun kama wasu mutane uku daga cikin waɗanda su ka yi garkuwa da ƴan makarantar sakandiren Bethel ta Kaduna.

Rundunar ce ta bayyana kanma mutane ukun a Abuja helkwatar rundunar ta ƙas a yau.

A yayin holen mutanen sun ce su 25 su ka yi garkuwa da ɗaliban sama da 100 a makarantar.

Guda daga cikin waɗanda  aka kama ya ce an bashi naira dubu 100 bayan sun yi garkuwa da mutanen.

Kakakin ƴan sandan Najeriya CP Frank Mba ne ya yi holen mutane ukun wadanda aka kama sanye da kayan sojoji.

Bayan garkuwa da ɗaliban sama da 100 an saki wasu daga ciki bayan biyan kudin fansa.

An saki sama da ɗalibai 50 bayan biyan kudin fansa da aka biya.

A halin yanzu akwai sama da ɗalibai 20 daga cikin daliban makarantar waɗanda su ke a hannun ƴan bindigan.

Sama da watanni biyu ɗaliban su ka shafe a hannun yan bindigan bayan da aka saki wasu daga baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: