Fadar shehun Borno ta gudanar da taron wayar da kan al’umma a kan yadda za su karɓi tubabbun mayaƙan Boko Haram idan sun shiga cikin su.

Taron da aka gudanar a ranar Talata hadin gwiwa da hukumomion majalisar dinkin duniyakamar UNDP da UNICEF.
An shirya taron ne musamman domin wayar da kan al’umma yadda za su rungumi tubabbun mayaƙan Boko Haram da su ka ajiye makaman su.

Wannan shi ne karo na farko da fadar ta shirya taro ganin cewar a na ci gaba da samun ƙarin mayaƙan Boko Haram da s ke tuba tare da ajiye makaman su.

Fadar ta ce ci gaba ne ganin yadda ake samun mayaƙan na baro daji tare da ajiye makaman su don ci gaba da rayuwa a cikin al’umma.
Wasu mutanen na ganin abin da kamar wuya ganin cewar mutanen na cikin fushi na halin da su ka jefa sun a kashe iyaye, ƙanne, yayye da ƴaya da mata.
Fiye da shekaru 12 kenan ake fuskantar rikicin mayaƙan Boko Haram musamman a arewa maso gabashin Najeriya wanda har yanzu ake ci gaba da ƙoƙarin saman da zaman lafiya a yankin.