Bayan dogon nazari da jarumi kuma mai ba da umarni Ibrahim Bala ya yi a ka matakin hukumar tace fina-finai ta yi na daina ɗaukar fim mai ɗauke da ta’addanci, jarumin ya ce fassarar Indiya-Hausa ne ke nuna ta’addanci kai tsaye.

A wata zantawa da Mujallar Matashiya ta yi da jarumin ya ce fassara da ake yi ita ke koyar da ta’addanci ba fina-finan Hausa ba.

Jarumin ya ce kyautuwa ya yi a dajtar da tace fina-finan da ake fassara wa domin su su ke koyar da yadda ake yin ta’addanci, daba, kace da garkuwa da mutane.

A wata zantawa da jarumin ya yi da mu a baya, ya ce ya kamata hukumar ta ƙarfafi masu yin fina-finan Hausa wajen ci gaba da fina-finan domin su na koyar da tarbiyya ne.

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ce ta dakatar da ɗaukar duk wani shirin fim dake nuna yadda ake garkuwa da wani aiki na ta’addanci.

A yayin da mu ka zanta da mai shirya fim ɗin A Duniya Tijjani Asase, ya ce ya na goyon bayan dokar kuma za su yi biyayya ga hukumar a bisa matsayar da ta ɗauka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: