Rundunar sojin Najeriya ta ce a halin yanzu fiye da mutane dubu takwas ne su ka tuba tare da ajiye makaman su daga ƙungiyar Boko Haram.

Hukumar ta ce mutanen sun ajiye makaman su tare da miƙa kan su ga jami’an tsaro da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Tubabbun mayaƙan da su ka tuba na ajiye makaman su tare da kai kan su ga jami’an tsaro.

Daga cikin mayaƙan mafi yawa sun je tare da matan su da yaƴan su kuma akwai ƙananan yara a ciki.

A halin yanzu gwamnatin jihar na kula wa da tubabbun mayaƙan kafin sake barin su shiga cikin jama’a.
Kwamishinan yada labaran jihar Baba Ƙura Abba ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da tantance su a wajen da ta killace tubabaun mayaƙan.
An fara samun masu ajiye makaman su daga cikin mayaƙan Boko Haram tun bayan mutuwar tsohon shugaban ƙungiyar Abubakar Sheƙau.
Mayaƙan Boko Haram da na ISWAP sun bayyana hadewar su sai dai an ci gaba da samun mutanen da ke barin ƙungiyar tare da kai kansu ga jami’an tsaro.