Rundunar yan sanda a Katsina sun kama wasu mata uku da ake zargi da kai wa ƴan bindiga man fetur a cikin daji.

An kama Dija Umar mais hekaru 50 sai Umma Bello mai shekaru 45 da kuma Nusaiba Muhammad mai shekaru 16 a duniya.

Matan da aka kama baki ɗayan su yan Malali ne a ƙaramar hukumar Katsina jihar Katsina.

Kakakin ƴan sandan jihar Isah Gambo ya bayyana cewa, matan na zuba man fetur din sannan su ɓoye shi a cikin jakar su sannan su kai wa ƴan bindigan.

An kama waɗanda ake zargi a ranar Alhamis da yamma yayin da su ke ƙoƙarin shiga cikin dajin Jibia don kai wa yan bindigan man fetur.

Tuni kwamishinan yan sandan jihar ya bayar da umarnin fara bincike a kan waɗanda ake zargi bisa laifin da su ka aikata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: