Rundunar yan sanda a jihar Imo ta sun kama wasu mata da miji bisa zargin kashe ɗan cikin su mai shekaru ashirin a duniya.

An kama Lambert Osundu da matar sa Racheal bayan sun kashe ɗan nasu Chukwuebuka sannan su ka binne shi da kan su a cikin gidan su.

An yi zargin ma’auratan sun kashe ɗan nasu bisa zargin taurin kai da ɗan nasu ke da shi.

Al’amarin ya faru a ranar 14 ga watan Satumban da mu ke ciki kuma sun kashe shi ne ta hanyar duka sannan su ka binni shi..

Kakakin yan sandan jihar Mike Abattam ya ce sun gudanar da bincike tare da kama mutane biyu bayan samun bayanai daga mazauna unguwar.

Rundunar na ci gaba da bincike don gano dalilin hakan sannan bayan sun kammala bincike a kan su za su gurfanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: