Rundunar yan sanda a jihar Kaduna sun yi nasarar daƙile wani hari da masu garkuwa su ka kai a Zariya.

Ƴan sanda sun kai ɗaukin gaggawa kuma sun samu nasarar kashe guda daga cikin masu garkuwa da mutane.
Kakakin yan sandan jihar ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da cewar ƴan bindigan sun shiga garin ne a safiyar yau kuma su na da yawa sai dai sun samu nasarar daƙile harin.

Da dama daga cikin ƴan bindigan sun gudu dauke da raunin harbin Bindiga.

Kakakin ya yi kira ga mutanen yankin da su lura a kan duk wani da aka ganshi dauke da raunin harbi, tare da sanar da jami’an tsaro.
Haka kuma ƴan sandan sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da satar shanu ciki har da wasu shanu da aka samu a hannun su.
An kama mutanen a yankin Kafancan ta jihar Kaduna kuma akwai wani Hussaini Damina wanda tuntuni rundunar ke neman sa ruwa a jallo.
Rundunar ta ce Hussaini Damina ƙasurgumin mai garkuwa da mutane ne kum sun kama su a ranar Lahadi yayin da su ke ƙoƙarin kai wasu shanu zuwa yankin da ba su kai ga ganowa ba.
Tuni rundunar ta ci gaba da gudanar da bincke domin samun wasu bayanai daga mutanen da aka kama.