Gwamnonin arewacin Najeriya sun gudanar da taro a yau a domin tattauna batun harajin VAT wanda wasu gwamnonin jihohin ke karɓa a maimakon gwamnatin tarayya.

A ranar Litinin ƙungiyar gwamnonin arewa su ka gudanar da taron a Kaduna a kan batun karbar harajin VAT.
Gwamnatin tarayya ce ta ce babu wanda ke da ikon karɓar harajin bayan ita, sai dai wata kotu a jihar Rivers ta ce gwamnonin jihohi na da ikon karɓar harajin.

Taron da aka yi a Kaduna ya samu jagoranci daga shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa Simon Baƙo Lalong.

Hukumar tattara haraji a Najeriya FIRS ta shigar da ƙara a kan yada wasu gwamnonin kudancin ƙasar ke ƙoƙarin mayar da karbar harajin ƙarƙashin ikonsu.
Tuni gwamnatin jihar Legas da Rivers su ka tabbayar da karbar harajin ƙarƙashin ikon su.