Rundunar ƴan sanda a Legas sun kama mutane 43 bisa zargin kashe wani babban jami’in su a jihar tare da ƙwato bindigu daga hannun mutanen.

An kashe wani baturen yan sanda yayin da su ka kai sumame da tawagarsa wani yanki a ƙoƙarin su na tabbatar da dokar hana hawa manyan titunan jihar.

A yayin da jami’in da tawagarsa su ka kai sumamen, mutane a yankiin sun kwace bindigun jami’an, sai dai kwamishinan yan sandan jihar ya ce an kwato bindigun da aka kwace daga hannun jami’an.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Hakim Odumosun ya bayyana rashin jami’in a matsayin babban rashi da rundunar ta yi a jihar.

Rundunar ta zargi masu hayar babur da aka fi sani da achaɓa da kashe jami’in sai dai masu hayar babura a jihar sun nesanta kansu da kashe jami’in.

Haka kuma sun sha alwashin zurfafa bincke tare da gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu bayan sun kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: