Aƙalla mutane 20 ne su ka rasa rayuwakan su sakamakon luguden wuta da jirgin sojin saman Najeriya ya yi a kan wasu masunta a Borno.

Jirgin ya yi luguden wutar ne a Kwatar Daban Masara da ke iyakar Chadi.

Wani shaida ya tabbatar wa da APF cewar al’amarin ya faru a ranar Lahadi.

A baya sai da rundunar sojin ta yi luguden wuta a jihar Yobe a nan ma mutane da dama sun mutu.

Sai dai rundunar ta ce jirgin ya yi kuskure ne hakan ta faru, a danganeda wannan lamari kuwa ba su magantu a kai ba har lokacin da mu ke kammala wannan labari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: