A safiyar yau wasu mabiya mazahabar shi’a a Abuja sunsha da ƙyar yayin da suka yi kiciɓis da sojoji.

Al’amarin ya faru ne a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna yayin das u ke yin tattaki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar sojojin sun daki wasu daga cikin mabiya mazahabar shi’a yayin da su ke yin tattaki a babban birnin tarayya Abuja.

An kama wasu daga ciki mabiya mazahabar shi’a daga cikin waɗanda su ka yi tattakin a yau.

Wasu daga cikin mabiya mazahabar shi’a sun gudu zuwa wata tashar mota sai dai sojojin sun shiga tashar tare da kama wasu das u ka gano mabiya shi’a ne.
Gwamnatin tarayya ta dakatar da duk wata zanga-zanga ga mabiya tun bayan gurfanar da shugaban su Ibrahim Zakzaky a gaban kotu.
Tuni kotu a Kaduna ta bayar da umarnin sakin sa tare da wanke shi a bisa zargin da ake yi masa shi da matar sa.