Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje zai samar da hukumar yaki da barace-barace a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar gamayyar ƙungiyar ƙungiyoyi masu zaman kansu a fadar gwamnatin.

“Ba za mu zura ido mu naɗe hannayenmu muna kallo rayuwar yara na lalacewa a banza ba” inji Ganduje.

Hakan na zuwa ne yayin da ake zaman majalisar zartarwa ranar Talata.

Gwamnatin za ta samar da hukumar ne domin yaki da barace-barace wanda hakan ke kara ta’azzara a jihar.

Sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya fitar,  gwamna Ganduje ya ce wulaƙantar da yara ne a barsu su na bara a kan titunan jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: