Hukumar sadarwa a Najeriya NCC ta sanya ranar 31 ga watan Oktoban da za a shiga a matsayin rana ta ƙarshe da aka bai wa mutane dama don hada layukan wayarsu da lambar ɗan ƙasa.

Daraktan harkokin jama’a a hukumar Dr. Ikechukwu Adinde y ace nan ba da jimawa ba za a daina bai wa mutanen da ba su hada lambar da katin ba damar gudanar da wasu abubuwan da su ka shafi gwamnatin ƙasar.
Daga cikin abubuwan da za a Diana bai wa mutane dama akwai lasisin tuki da kuma fasfo na fita ƙasashen waje.

Sama da sau uku ana ƙara wa’adin hada lambar ɗan ƙasa da layukan wayar salula.

Hukumar ta samar da tsarin ne domin taimaka wa tsaron ƙasar.
Najeriya na da mutane sama da miliyan 200 sai dai ba a bayyana adadin mutanen da su ka haɗa lambar da layukann wayar su ba zuwa yanzu.
Hukumar ta sake jaddada wa’adin da ta sanya na 31 ga watan Oktoba a matsayin ranar ƙarshe da aka bai wa mutanen ƙasar dama don haɗa layukan wayar su da lambar ɗan ƙasa ta NIN.