Aƙalla mutane 30 aka kashe yayin da mutane ke barin muhallin su a sakamakon hare-haren yan bindiga a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja.
Mutane a ƙauyen Sarkin Pawa na jihar Neja na guduwa a sakamakon harin da yan bindiga su ka kai tare da sace mata bakwai a kauyen Sabon Kachiwe.
Yayin da ƴan bindigan su ka je garin sun fara harbin mutane sannan su ka ƙone ƙauyen kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida hakan.
Sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin wanda y ace an kai harin ne a ƙauyuka uku na ƙaramar hukumar Munya ta jihar.
Ya ce an kashe wasu mutane goma kuma aka ƙone su, an kasa samun jami’an tsaro don sanar da su halin da ake ciki a garin sakamakon katse layukan sadarwar waya a yankin.
Ƴan bindigan su tafi da mata bakwai kuma ba a san inda su ka nufa da sub a.
Jihar Neja na daga cikin jihohin da ake fama da rikicin yan bindiga wanda abin ya ta’azzara.