Aƙalla sojoji biyu yan bindiga su ka kashe yayin da su ka jikkata wasu da dama a wani hari da su ka kai Kagara ta jihar Neja.

Gwanan jihar Abubakar Sani Bello ne ya sanar da haka yayin da ya je duba wadanda su ka samu rauni a babban asibiti da ke Minna babban birnin jihar.

Gwamnan y ace wannan abin takaici ne kuma ba za su bari ya ci gaba da ɗorewa ba.

Ya ƙara da cewa akwai wasu ƙarin jami’an da su ka samu raunii baya ga guda 12 da ya je duba lafiyar su a asibitin.

Sauran sojojin da su ka samu rauni an kais u asibitin Kaduna don ci gaba da kula da lafiyar su, sai dai gwamnan bai bayyana adadin wadanda ke asibitin Kaduna ba.

Ya ce wannan abin takaici ne kuma yaƙi da ta’addanci ya iya jami’an tsaro kaɗai ya shafa ba har sauran al’umma baki ɗaya ya shafa.

Haka kuma gwamnan ya duba wasu wadanda su ka samu rauni daga harin ƴan bindiga a watannin baya,sannan ya tallafa musu da kudi don rage raɗadin abi  da ya dame su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: