Shugabannin Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin bai wa matasa dama a dama da su a bangarorin siyasa da sauran madafun ikio.

Shugabana ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi na ranar samun yancin kai a Najeriya shekaru 61.
Shugaban yay i wasu maganganu da s ka danganci al’amuran da su ka shafi ƙasar kamar batun tsaro, cin zarafi da fyade da kuma tattalin arziƙin ƙasa.

Shugaba Buhari ya buƙacin yan Najeriya da su dinga hada kan su don ci gaba da kasancewar Najeriya ƙasa ɗaya al’umma ɗaya.

Najeriya tga cika shekaru 61 da samun ƴancin kai tun bayan da turawan Burtan kiya su ka miƙa ragamar mulki ga yab ƙasar.
Babban taron da aka yi a Abuja ya samu halartar anyan jami’an gwamnatin ƙasar da tsofaffin shugabannin ƙasar Najeriya.