Gasar na da dokoki kuma a kan iya cin kyautuka da kofi ga waɗanda su ka yi nasara.

A Najeriya za a fara wasan gasar mari a watan Oktoban da mu ke ciki.

Babban darakta a hukumar wasannin motsa jiki Abdulrahman Orosanya ne ya bayyana haka a Legas.

Ya ce za a fara wasan gasar marin ne a watan da muke ciki sai dai ba a tsayar da tsayayiyar ranar da za a fara wasan ba.

Za a tsara wasan  marin tare da tsara gudanar da tsarin cin gasar kofin wanda za a yi duka a jihar Legas.

Daraktan ya ƙara da cewa gasar marin sabon wasa ne da ya shigo Najeriya wanda aka sabunta shi a ƙasar Rushiya kuma ya shahara a kasar Amuruka da sauran ƙasashen turai.

An zaɓo gasar marin ne tare da shigar da shi cikin tsarin wasannin motsa jiki wanda za a tsara cin kyautuka da gasa a ƙarƙashin sag a waɗanda su ka yi nasara.

Yadda gasar ta ke shi ne mutane biyu za su su dinga marin junan sub a tare da saka wani abu a hannun ko fuskarsu ba.

mutane biyu ne za su fuskanci junan su sai kuma alƙalin wasa a tsakiya sannan a bayar da loacin ga kowanne ɓangare, wanda ya yi abinda ake buƙata a kan lokaci shi ne ya yi nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: