Wasu da ake zargin yan ta’addan ƙungiyar IPOB ne sun kai hari ofishin yan sandan farin kaya a jihar Anambara.

Maharan sun kai harin ne ranar Lahadi tare da kai wani harin ofishin hukumar kiyaye afkuwar haɗdura ta ƙasa a jihar.
A na zargin wasu mutane biyu sun mutu a sakamakon hare-haren da yan ta’addan su ka kai.

Ƴan bindigan sun fara harbe harben iska sannan su ka farwa ofisoshin jami’an.

Sun kjai harin ne a kan ababen hawa kuma harbe-harben da su ka yi ne ya figita jama’a wanda ya sa su ka tsere don tsira da rayuwar su.
Rundunar yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin kamar yadda kakakin yan sandan jihar DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar.
Ya ce al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe biyu na rana.
Tuni aka aike d dakarun yans anda wurin da abin ya faru don samar da cikakken tsaro, kuma ya ce cikakken bayani zai zo daga baya bayan sun kammala bincike a kai.