Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa a Najeriya sun bayyana janye yajin aikin da su ka tsunduma yi sama da watanni biyu.

Babban sakataren ƙungiyar ne ya sanar da haka a ranar Lahadi ya na mai cewa likitocin za su koma bakin aikin su a ranar Laraba.
Sanarwar ta ƙara da cewar tsaikon da aka samu wanda ya haifar da yajin aikin ya faru ne sakamakon rashin cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da ɓangaren gwamnatin tarayya.

Bayan koma wa bakin aikin su za a sake zama tsakanin su da bangaren gwamnatin makwanni shida masu zuwa a nan gaba.

Ƙungiyar ta yanke wannan hukunci ne bayan cimma daidaito da aka yi a ƙungiyar.
A ranar 2 ga watan Agusta ne ƙungiyar ta tsunduma yajin aikin wanda ta ce ta fara ne saboda ƙin mutunta yarjejeniyarsu da gwamnatin Najeriya sama da kwanaki 100.
Ƙungiyar na son a biya haƙƙoƙin mambobin ta da kuma wasu buƙatu wanda har yanzu aka gaza cimma matsaya.