Connect with us

Labarai

Ƴan Boko Haram Sun Umarci Mutane A Neja Su Aurar Da Ƴaƴansu Mata A Shekara 12

Published

on

Mayaƙan Boko Haram a jihar Neja sun shimfiɗa wasu sharuda a yankunan da su ka mamaye.

Mayaƙan sun buƙaci al’ummar wasu ƙauyuka da su janye yaƴan su daga makarantun boko.

Haka kuma mayaƙan sun buƙaci mabiya addinin musulunci da na  kirista da su aurar da yaƴasu mata a yayin da su ka cika shekaru 12 a duniya.

Ƴan Boko Haram sun mamaye wasu ƙauyuka da dama a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.

Tun a baya gwamnan jihar ya bayyana cewar mayaƙan na kafa sansani a dazukan jihar kafin daga bisani su fara shiga garuruwa a jihar.

A na zargin mayaƙan Boko Haram na ɓoye a dazukan Kaduna Neja da yayin da ake zargin akwai wasu a jihar Sokoto kamar yadda sanarwar rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewar su su ka kai wa jami’an ta hari a jihar.

a na zargin mayaƙan Boko Haram sun mamaye ƙauyuka da dama a ƙarananan hukumomin Shiroro, Munya, da kuma karamar hukumar Rafi.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Rufe Dukkanin Asusun Ajiyar Bankuna Na Gwamnatin Jihar Kano

Published

on

Babbar kotun tarayya da ke zamanta Jihar Kano ta bayar da umarnin rufe dukkan asusun bankunan gwamnatin Jihar Kano bisa kin biyan diyyar rusau din da gwamnatin ta yi a wasu gurare a Jihar.

Kotun ta rufe asusun gwamnatin ne akalla 24 ciki harda na babban bankin Kasa CBN.

Alkalin kotun mai shari’a I.E Ekwo shine ya bayar da umarnin bayan shigar da karar da masu shaguna da ‘yan kasuwa suka shigar gaban kotun bisa rusau din da aka yi musu.

Kotun ta ce ta dauki matakin hakan ne bisa kin bin umarnin kotun da gwamnatin ta yi na bai’wa ‘yan kasuwar diyya.

Kotun ta kuma bai’wa wadanda ake Kara umarnin su bayyana agabata domin jin dalilin da ya sanya suka bijirewa umarnin nata.

Kazalika kotun ta ce matukar wadanda ake Kara basu bayyana ba a gabanta za ta cire naira biliyan 30 domin biyan diyya ga ‘yan kasuwar.

Bayan bayar da umarnin kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2024 mai kamawa.

Rufe asusun na zuwa ne sakamakon rusau din da gwamnatin ta Kano ta yi a wasu guraren tun bayan hawan ta kan mulki bisa zargin cewa an yi su ba bisa ka’ida ba.

 

Continue Reading

Labarai

Sheikh Ahmad Gumi Yayi Allah Wadai Da Kashe Al’umma Masu Taron Maulidi A Kaduna

Published

on

Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi Allah-wadai da hallaka mutane da jirgin soji yi a garin Tudun Biri a Jihar Kaduna.

Malamin ya bayyana hakan ne ta cikin wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Facebook, Gumi ya ce lamarin abin takaici ne da ke yawan faruwa a yankin Arewacin Kasar.

Sheikh Ahmad Gumi ya kara da cewa ana maida Jihohin Arewacin Kasar tamkar zirin Gaza, kamar yadda sojojin Israila su ke hallaka mutanen kasar Falasdin.

A jawabin na Gumi ya zargi hukumomin Kasar da nufi mara kyau ga mutanen Kasar, tare da yin kisan kare dangi da ganganci ga al’ummar da ke kauyukan Arewa.

Gumi ya ce hakan ba zata taba yuwuwa ba jirgin yayi kuskure wajen sanya bam ga masu fararen kaya ba.

Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa akwai wata a kasa wajen sanyawa masu taron mauludin bom din da jirgin yayi.

Continue Reading

Labarai

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayarwa Da Peter Obi Martani Akan Sukar Shugaba Tinubu

Published

on

Fadar shugaban kasa ta yiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party ga Peter Obi raddi akan yadda ya ke sukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Martanin ya fito ne daga ofishin Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ta bakin mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha a ranar Talata.

Sanarwar ta zargi Peter Obi da bata gwamnatin Tinubu bisa rashin nasarar da ya samu a lokacin zaben kasar.

Sanarwar ta ce Peter ya yi amfani da zargin zuwa taron COP na 28 da shugaban ya tafi da mutane 1411, domin cimma wata manufa tasa ta siyasa ta hanyar yaudara.

Sanarwar ta ce Obi ya shafe tsawon lokaci ya na sukar gwamnatin ta Tinubu domin ya nuna cewa ya na kishin kasa, kuma ba gaskiya yake fada ba a kalamannasa.

Martanin na zuwa ne bayan da Peter Obi ya soki gwamnatin tarayya akan kudin da aka kashe wajen zuwa taron dumamar yanayi na COP karo na 28 da kuma shirin gyara gidan mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: