Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari za gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2022 a ranar Alhamis.

Shugaban zai gabatar wa majalisar dattijai kasafin a zauren majalisar wanda zai bayar da damar gudanar da ayyuka a shekarar mai zuwa.
Mataimakin shugaban majalisar ne ya gabatar da haka a yayin da yake bayanin shirye-shiryen abubuwan da za a gudanar a zaman majalisar na gaba.

Kasafin kudin da ake sa ran zai gabatar za a duba shi tare da neman amincewar majalisar domin zartar da shi cikin doka.

A kwanakin baya ne dai majalisar ta amince wa shiugaban don ciwo bashin maƙudan kudade wanda zai cike giɓin ayyukan da aka tsara gudanar wa a shekarar da mu ke ciki.
Shugaban majalisar ya buƙaci kwamitin tsare-tsare da kasafi da su fara shirye-shirye domin karbar kasafin tare da fara bita a kan sa.