Al’ummar yankin Kuryar Madaro da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda na cikin wani hali bayan ƴan bindiga sun kashe mutane tare da ƙone ababen hawa a garin.

Yan binduga sun shiga garin da misalin ƙarfe 10 na daren Talata sannan su ka hallaka mutane da dama tare da cinnawa gidaje da ababen hawa wuta.

Bayan shigar ƴan bindigan sunshafe awanni da dama a yankin su ba tare da an kai wa mutanen ɗauki ba.

A halin da ake ciki an gano gawarwaki guda 19 yayin da ake ci gaba da bincike a kai.

Ƴan bindigan da su ka kai harin sun sace abinci sannan su ka kore dabbobi masu yawa.

Wani ya shaidawa jaridar Daily Trust cewar ƴan bindigan sun ƙona gidaje 13 sai ababen hawa guda 16 ciki har da motar yan sanda.

An katse hanyar sadarwar wayar salula a Zamfara domin kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga wanda su ka shafe lokaci su na ta’addancin kashe mutane a ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: