Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2022.
Shugaban ya gabatar da kasafin a zauren majalisar dokokin Najeriya yau Alhamis.
Ya gabatar da kasafin kuɗin da ya kai naira Tiriliyan 16.39 kuma ake sa ran za a samu naira tiriliyan 10.13 daga haraji a ƙasar.
Tuni majalisar zartarwa a Najeriya ta amince da kasafin kuɗin yayin zaman majalisar na jiya Laraba.