Gwamnatin jihar Zamfara ta ce a halin yanzu akwai yan gudun hijira sama da 700,000 wadanda ke zaune a sansani daban-daban na jihar.

Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ne ya sanar da haka a yayin ganawarsa da yan jarida wanda ya ce sun bar muhallin su ne a sanadin rikicin yan bindiga da ya addabi jihar.

Gwamnatin ta karɓi mutane 185 wadanda ƴan sanda su ka karba bayan yin sulhu da ƴan bindiga a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Kabiru Balarabe ne ya sanar da haka ya na mai cewar gwamnatin jihar za ta ci gaba da matsawa yan bindigan har lokacin da za su saduda da kan su.

Guda cikin mutanen da aka kuɓutar ta bayyana cewar mutane 17 daga cikin su sun mutu a sansanin yan gudun hijirar sakamakon wahala da rashin abinci.

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya ce bisa matsawa da ƴan bindgan ke samu da rashin samun abinci ya sanya su ke wahalar gudanar da ta’addanci a jihar.

Jihar Zamfara ta kasance cikin jihohin da ƴan bindiga su ka addaba tare da kashe mutane sace ababen dabbobi da kuma kayan amfani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: