Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware naira miliyan 104,532,705 domin yaƙi da kalaman batanci da labaran ƙarya a ƙasar.

Hakan na cikin kasafin kudin shekarar 2022 wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar Alhamis.

Minsitan yada labarai da al’adu a Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce Najeriya ta ɗauki ɗamarar yaƙi da kalaman ɓatanci a ƙasar.

A yayin da yake ganawa da kamfanin dillacin labarai na ƙasa NAN minista Lai Mohammed ya ce hukumar lura da kafafen yada labarai a ƙasar ta fitar da sabuwar dokar hana tallata ayyukan ƴan bindiga a gidajen talabiji.

Haka kuma kuɗin da aka ware za a yi amfani da su wajen yaƙi da labaran karya, kalaman ɓatanci da kuma tallata wasu muggan ayyuka.

A baya gwamnatin ƙasar ta dakatar da amfani da shafin Tuwita a ƙasar bayan zargin taimakawa wani ɓangaren ƙasar wanda gwamnatin ta ce hakan na iya kawo rarrabuwar kai da kuma rashin zaman lafiya.

Sai dai shugaban ya ɗage wannan takunkumi bisa wasu sharuda da ya zayyana a cikin jawabinsa na ranar samun yancin kai da Najeriya ta yi shekaru 61.

Leave a Reply

%d bloggers like this: