Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaɗu a bisa rashin dattijo Alhaji Muhammad Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss.
A cikin saƙon ta’aziyya wanda ya aike ta hannun babban sakataren yada labaran sa Malam Abba Anwar, Ganduje ya ce rashin sa babban giɓi ne wanda maye gurbinsa sai an yi da gaske.
Gwamna Ganduje ya ce samun irin Alhaji Aminu Adamu Abba Boss a cikin al’umma babban al’amari ne amma ya tafi a lokacin da al’umma ke buƙatar sa.
“Tabbar ya rasu, a lokacin da miliyoyin al’umma ke buƙatar sa, sai dai wanda ya karɓe shi ya fi mu son shi” a cewar gwamna Ganduje.
Ganduje ya bayyana Abba Boss a matsayin shugaba, kuma jagora wanda ya ke sadaukar da lokacin sa, dukiyarsa, da lafiyarsa don hidimtawa al’umma tare da samar da ci gaba a jiha da ma ƙasa baki ɗaya.
“Abba Boss mutum ne mai tsoron Allah, gaskiya da riƙon amana” a cewar gwamna Ganduje.
Gwamnan ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalai ƴan uwa da abokan arziƙi da dukkanin al’umma a madadin gwamnatin tare da fatan Allah ya ji ƙan sa da rahama.
Abba Boss ya rasu a ranar Asabar da daddare bayan ya sha fama da jinya.
Ya rasu ya bar mata biyu da yaya maza da mata da jikoki daga cikin iyalan sa.