Alhaji Muhamamd Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss guda ne cikin jama’ar da ke talafe da rayuwar dubban mutane tare da ƙoƙarin ceto da yawa daga cikin don inganta rayuwar su.

Ya kasance ɗan kasuwa kuma manomi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa jama’a da addinin musulunci.
Mutum ne da ya ɗauki nauyin marayu wajen ciyar da su shayar da su da ma tufatar da su har ma da harkar ilimin su.

Marasa lafiya da dama ke biyawa kuɗin magani ba tare da sun san wanene ya yi ba.

Kyautata mutane ya ke yi musamman idan ya fuskanci mutum na da jajircewa wajen neman na kansa ko karatu.
Ya samar da tsarin ciyarwa don marayu da iyayen marayu da ma marayun wanda ke amfana daga lungu da saƙo na jihar Kano.
Ya na daga cikin ɗabi’un sa kyautata wa tare da mutunta Ɗan’adam wajen ganin an samar da ci gaba ta hanyar hada kai.
Mutum ne mai kishi tare da ƙoƙarin zaburar da mutane masu kishi wanda hakan ya sa ya ke kulawa da mutane da dama musamman masu ƙaramin ƙarfi wajen ganin sun tsaya da ƙafarsu.
Abba Boss ya zamto guda ɗaya tilo da ake kwatance da alherinsa a ciki da wajen yankin sa.
Kiyaye lokaci, tabbatar da adalci da gaskiya na daga cikin abubuwan da ya ke bai wa muhimmanci.
Alhaji Aminu Adamu jajirtacce ne wajen ganin an samawa talaka ƴanci wajen gudanar da tsarin rayuwa tare da ingantata.
Ya na daga cikin mutanen da ke amfani da kuɗaɗen sa don wayar da kan jama’a ta yadda za su san yancin su.
Abba Boss na daga cikin mutanen da su ka ja hankalin gwamnati yayin da aka sanya dokar kulle ta KORONA har aka sassautata wanda miliyoyin ƴan Najeriya su ka fita daga ƙangin da su ke ciki a wancen lokaci.
Hidimarsa ba ta tsaya a nan ba sai da ci gaba da yin amo don ganin ya ja hankalin gwamnati a kan yadda ake tsadar kayan masarufi tare da jan hankalin ƴan kasuwa don ganin sun rangwantawa talakawa.
Wannan kaɗan kenan daga cikin kyawawan halayen da marigayi Alhaji Muhammadu Aminu Adamu Abba Boss ya bari kuma mutane ke ƙoƙarin koyi da shi.
Ya rasu a ranar Asabar 09 10 2021 ya bar mata biyu da ƴaƴa maza da mata daga cikin iyalan sa akwai jikoki a ciki.
An yi jana’izarsa ranar Lahadi 10/10/2021 a gidansa da ke unguwar Gama (B).
Allah ya ji ƙansa da rahama idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani amin.
Abubakar Murtala Ibrahim
(Abban Matashiya)
10/10/2021