Majalisar malamai a Kano ta rushe shugabancin Malam Ibrahim Khalil tare da maye gurbin sa da Farfesa Abdalla Saleh Pakistan.

Majalisar ta zargi Malam Ibrrahim Khalil da amfani da su don cimma buƙatar karan kan sa.

A yayin taron ƴan jarida da aka gudanar a cibiyar ƴan jarida da ke Kano, jagoran malamai a madadin malaman Kano Ustaz Saifullahi Adam ASSUDANI ya bayyana cewar, rashin bayar da fatawa a kan daidai tare da kaucewa mazahabar maikiyya na daga cikin dalilan da su ka sanya su ka rushe shugabancin malam Ibrahim Khalil.

Ya ƙara da cewa, shugabancin na riƙo ne kuma za su samar da tsarin karɓa karɓa tare da tsara wa’adi domin tabbatar da nasarar malamai da kuma ilimin da za su dinga bai wa al’umma.

Gamayyar malaman wanda su ka samu wakilci daga ƙungiyoyin Izala, Tijjaniyya da kuma ɗariƙar Ƙadiriyya sun yi mubaya a da sabon shugabancin da aka naɗa.

Gamayyar malaman sun sanar da cewar sun aika ƙorafinsu zuwa ga malamin a kan abubuwan da su ke tuhumar sa a kai, amma bai mayar musu da amsa a kana bin da su ke thumar sa ba.

Malamai daga ƙananan hukumomi a Kano ne su ka halarci taron wanda aka yi a yau, tare da wakilc daga hukumar Hisbah a Kano.

Malaman sun nemi goyon bayan gwamnatin Kano don amincewa da sabon shugabancin da su ke bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: