Babbar kotun jihar Kano ƙarƙashin mai shari a Sulaiman Baba Namallam ta yanke wa wani Usman Usman hukuncin shekaru 14 a gidan gyaran hali.

An yake wa Usman hukuncin ne bayan samunsa da aikata fyaɗe a kan wata yarinya mai shekaru 13 a duniya.

Usman mai shekaru 50 a duniya ya aikata laifin da ya ci karo da sashe na 283 na kundin doka.

An zargi mutumin da aikata laifin a watan Afrilun shekarar 2016, sannan an yanke hukuncin bayan gabatarwa da kotu shaidu wanda ta tabbatar da cewar mutumin ya aikata laifin.

Kotun ta umarci wand ake zargi da biyan wadda yay i wa fyaɗen diyyar naira dubu ɗari uku ba tare da zaɓi ba.

Mutumin mazaunin unguwar Walawai a ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano zai zauna a gidan gyaran hali tsawon shekaru 14 tare da biyan diyya ga wadda yay i wa fyaɗen.

Tuni wasu jihohi a arewacin Najeriya su ka amince da hukuncin kisa a kan duk wanda aka smau da aikata fyaɗe a jihohin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: