Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Jigawa ta yi holen mutane 134 da ake zargin su da hannu wajen ta’ammali da haramtattun ƙwayoyi a jihar.

Shugaban hukumar a jihar Maryam Gambo Sani ce ta sanar da haka a yayin da ta ke gabatar da masu laifin a gaban ƴan jarida ranar Litinin.

Ta ce akwai wasu da dama daga cikin su waɗanda matasa ne ɗalibai kuma kashi 99 daga ciki maza ne yayin da aka samu mata biyu a ciki.

Dukkanin mutanen da aka kama an kamasu ne cikin makonni biyu.

Haka kuma akwai wasu shugabanniin gargajiya biyu daga cikin wadanda aka kama sai dai ba ta faɗi matsayinsu da kuma wurin da su ke mulka ko sunan su ba.
Ana zargin mutanen da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma siyar da su wanda ta ce sun kwato kayan maye na miliyoyin nairori.

Leave a Reply

%d bloggers like this: