Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun sace wasu ɗalibai a wata makaranta a Kaduna.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Litinin da daddare sannan su ka dinga harbe-harbe kai mai tsautsayi.

An kai hari makarantar Saint Albert Seminary ta garin Kogoma kuma su ka sace ɗalibai uku daga cikin ɗaliban makarantar.

Akwai wasu daga cikin ɗalibai wadanda su ka samu rauni kuma an kai su asibiti don duba lafiyarsu.

Wannan sabon al’amari ne da ya faru tun bayan hare-hare da yan bindiga ke kai wa makarantu a Kaduna.

An shiga da ɗaliban cikin daji kuma ba su nemi abin da su ke buƙata kafin sakin sakin ɗaliban ba.

Har yanzu akwai akwai sauran ɗalibai huɗu da ke hannun ƴan bindiga waɗanda aka sace a makarantar Bethel da ke Kaduna.

Ƴan bindigan na karɓar kudin fansa sannan su saki ɗaliban da ke hannun su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: