Zauren majalisar malamai sun yi watsi da tsige shugaban majalisar wanda wasu daga cikin malaman Kano su ka yi a ranar Litinin.

Wata wasiƙa wadda sakataren zauren majalisar Dakta Sa’id Ahmad Dukawa ya sanyawa hannu, sun ce su na nan a kan tsarin su na shugabanci ƙarƙashin Malam Ibrahim Khalil.

Zauren hadin kan malaman sun ce ba da yawunsu aka yi hakan ba, kuma ba sa goyon bayan wancen ƙudire na sauke shugaban Malam Ibrahim Khalil.

daga cikin ƴan kwamitin wanda su ka amince da shugabancin akwai, Farfesa Musa Muhammad Borodo, Khalifa Sheik Ƙaribullah Nasiru Kabara, Sheik Abdulwahab Abdalla, Shei Ibrahim Sheuhu Maihula, Farfesa Muhammad Babangida Muhammad, Dakta Bshir Aliyu Umar, Imam Nasir Muhammad Adam, da Dakta Ibrahim Mu’azzam Mai Bushira.

Zauren ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da ririta zaman lafiyarsu tare da kaucewa duk wani abu da ka iya haifar da rashin zaman lafiy a jihar Kano.

A ranar Litinin ne wasu daga cikin tsagen malaman Kano su ka bayyana sauke Sheik Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai tare da maye gurbinsa da Farfesa Abdallah Saleh Pakistan.

Malaman sun ce sun wakilci dukkanin ɓangarorin ɗariƙu uku na Tijjaniyya, Ƙadiriyya da  Izala a yayin taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: