Connect with us

Labarai

Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Sojoji Wuta A Zamfara

Published

on

Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun buɗewa sojoji wuta a ƙauyen Wanzamai da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Bayan buɗe wutar sun kashe sojoji biyar daga ciki yayin da su ka kwashe mkaman jami’an.

Wani da al’amarin ya faru a gabansa ya shaida cewar, ƴan bindigan sun buɗe wa sojojin wuta ne yayin da su ke kan hanya.

Al’amarin ya faru da misalin ƙarfe biyu zuwa uku na rana, daga bisani sojoji sun rufe hanyar wanda hakan ya haifar da tsaikon ababen hawa a babbar hanyar.

Wasu mutanen yankin sun ce su su ka taya ƴan sanda kwashe gawarwakin sojojin bayan da abin ya lafa.

Ƙaramar hukumatr Tsafe iyaka ce tsakanin Katsina da Zamfara.

An rufe kafofin sadarwa a Zamfara sama da wata guda domin kawo ƙarshen ta’addancin ƴan bindiga da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsawon lokaci.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Gwamnatin Borno Za Ta Dinga Biyan Daliban Jinya Da Ungozoma 30,000 Duk Wata

Published

on

Gwanatin jihar Borno ta sanar da fara biyan daliban jinya da ungozoma tallafin karatu ga kowanne dalibi har N30,000 duk wata a fadin jihar.

 

Gwamna Babagana Umara Zulum ya tabbatar da lamarin jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu yayin bikin kaddamar da tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin Borno a Maiduguri, babban birnin jihar.

 

A cewar jaridar Daily Trust, gwamnan ya tabbatar da cewa dalibai 997 da suka fito daga jihar ne zasu mori tallafin.

 

Ya kara da cewa tallafin an yi shi ne ga daliban lafiya domin karfafa musu guiwa da samar da wadatattun ma’aikatan lafiya a jihar.

 

Jawabin nasa ya nuna gwamantin za ta kashe jimillar N1.3b a kan daliban a matsayin tallafi.

 

Mai girma gwamnan ya kuma bayyana cewa tallafin ya shafi kudin makaranta da alawus da za a rinka basu duk wata.

 

A cewar gwamnatin, daliban zasu rinka karban alawus din ne daga shekarar da suka fara karatu har su kammala.

 

Gwamnan kuma ya yi alkawarin bada aiki nan take ga dukkan daliban da suka nuna bajinta a lokacin karatun nasu.

Continue Reading

Labarai

NDLEA Ta Lalata Haramtattun kwayoyin A Legas Da Osun

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar lalata haramtattun kwayoyi a jihohin Legas da Ogun.

Hukumar ta samu nasarar ne a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook, ta tabbatar da lalata jimillar kilogiram 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun kwayoyi da ta kama daga sassan jihohin Legas da Ogun.

Hukumar ta lalata haramtattun kwayoyin ne da ta kama a bainar jama’a a Badagry da ke jihar Legas.

Shugaban hukumar ta kasa, Mohamed Buba Marwa ya ce lalata haramtattun kwayoyi da aka kama ya biyo bayan umarnin kotu ne.

Buba Marwa ya yi kira domin samun karin goyon bayan jama’a kan kokarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da yi na dakile matsalar shan da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Marwa ya kara da cewa kwayoyin da suka kama nau’o’i ne daban-daban da suka hada da koken, kanabis da tramol.

Shugaban ya kuma mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya, shugabannin tsaro, malamai, kungiyoyi da sauran wadanda suka shaida lalata kwayoyin.

Continue Reading

Labarai

Babbar Kotun Tarayya Ta Jingine Dakatarwar Da Aka Yiwa Ganduje

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu nasara a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano.

 

Babbar kotun ta jingine dakatarwar da shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, suka yi wa tsohon gwamnan na Kano.

 

Alƙalin kotun, mai shari’a Abdullahi Liman ya umurci shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, kada su yi aiki da umurnin babbar kotun jihar na dakatar da Abdullahi Umar Ganduje.

 

Mai shari’a Abdullahi ya kuma ya hana duk waɗanda umurnin babbar kotun jihar ya shafa bin umurnin, har sai an saurari ƙarar da Ganduje ya shigar ta neman a yi masa adalci a saurari ɓangarensa.

 

Wannan umurnin dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan babbar kotun jihar ta amince da buƙatar shugabannin APC na mazaɓar Ganduje ta dakatar da tsohon gwamnan na Kano.

 

Shugabannin dai sun dakatar da Ganduje ne saboda zargin cin hanci da rashawa da almundahana da gwamnatin jihar Kano ke yi masa.

 

Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan Afrilu domin sauraren buƙatar da Abdullahi Umar Ganduje wacce lauyansa Jazuli Mustapha ya gabatar a gabanta.

 

Waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar sun haɗa da Haladu Gwanjo, Nalami Mai AC, Muhammadu Baiti, Danmalam Gata, Musa Lado, Laminu Sani Barguna, Umar Sanda, Auwalu Galadima da Abubakar Daudu. Sauran sun haɗa da rundunar ƴan sandan Najeriya, kwamishinan ƴan sandan Kano, hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), da hukumar kare farar hula (NSCDC)

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: