Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ƴan Majalisar Tarayya Da Na jiha Na goyon Bayan Ganduje A Zaɓen Shugabancin Jam’iyya Na Kano

Ƴan majalisar tarayya 20 ne su ka nuna goyon bayan su ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a yayin da ake gab da gudanar da zaɓen shugaban jam’iyyar APC a Kano.

Hakan ya bayyana ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda ya gudana yau a ɗakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin Kano kamar yadda babban sakaren yaɗa labaran gwamnan Malam Abba Anwar ya ruwaito.

Cincirondon yaƴan jam’iyyar nee su ka yi amanna da nuna goyon bayan gwamnan domin ci gaban jam’iyyar.

Daga cikin ƴan majalisar tarayyar har da shugaban masu rinjaye a majalisar Hon. Alasan Ado Doguwa.

Haka kuma akwai yan majalisar jiha 28 waɗanda su ka yi amanna da tare da ƙarfafar tafiyar gwaamna Ganduje a yayin da ake tinkarar zaben.

Sannan akwai Sanata Kabiru Gaya wanda shi ma ya halarci taron.

Dukkanin mutanen sama da dubu uku sun nuna goyon bayan su tare da tabbatar da cewar za su yi biyayya ga duk wani zaɓi da gwamnan ya yi a kai.

Gwamnan ya gode wa dukkanin mutanen da su ka yi mubbaya’a a gare shi a mataki daban-daban don ƙarfafa gwiwar tafiyar tsarin siyasar sa.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: