Kotun shari’ar musulunci da ke zaune a ƙofar Kudu ta buƙaci lauyoyin gwamnati su gabatar da shaidun da su ke da su a kan tuhumar da ake yi wa Sheik Abduljabbar Kabara.

Alƙalin kotun Ibrahim Srki Yola ne ya bayyana haka a yayin ci gaba da sauraron ƙarar da gwamnatin Kano ke yi a kan Abduljabbar Kabara.

Yayin zaman na yau, an samu saɓani tsakanin Abduljabbar da lauyoyin sa a kan shaidun da su ka gabatarwa kotu.

Lauyoyin sun janye buƙatar ɗaukaka ƙara sai dai su na buƙatar kotu ta sauke sauraron manyan lauyoyin gwamnati wanda ciki har da masu muƙamin SAN.

Alƙalin kotun Ibrahim Sarki Yola ya bayyana amincewar hakan, sai dai ya buƙaci lauyoyin da su ke ƙara su gabatar wa da kotu shaidun da ta ke buƙata.

Sannan kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga watan Oktoban da mumke ciki.

Gwamnatin Kano ce ta zargi Malam Abduljabbar da yin kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W da kuma yin kalaman tayar da fitina a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: