Ƴan sanda sun tabbatar da kai harin sai dai ba su bayyana adadin mutanen da su ka mutu ba.

Aƙalla mutane 12 ne su ka rasa rayukansu a sabon harin da yan bindiga su ka kai ƙauyen Sakajiki da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun kutsa kai cikin ƙauyen a ranar Alhamis da daddare sannan su ka ƙone shaguna 19 bayan sun kashe mutane.

Daga cikin motocin da yan bindiga su ka ƙona har da motar ƴan sanda guda biyu.

Wani shaida wanda abin ya faru a kan idon sa ya tabbatar da cewar ƴan sanda sun yi ƙoƙarin daƙile harin sai dai ƴan bindigan sun ci ƙarfin yan sandan sannan su na ɗauke da manyan makamai.
Rundunar ƴan sanda a jihar ta bakin kakakin ta SP Muhammad Shehu sun tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai bayyana adadin mutanen da su ka rasa rayuwarsu ba.
Muhammad Shehu ya ce yan sandan jihar na iya bakin ƙoƙarinsu kuma za su ci gaba da ayyukan stare rayuka, lafiya da dukiyoyin al’umma.
Haka kuma za su rubanya ƙoƙarinsu don ganin sun shafe tarihin ƴan bindiga a jihar Zamfara.