Rundunar ƴan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama mutane 138 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.
An kama mutanen wadnada su ka haɗa da ƴan fashi da makami garkuwa da mutane, fyaɗe da sauran miyagun ayyuka.
A yayin da yake jawabin lokacin da ya ke gabatar da masu laifin a gaban yan jarida, kakakin ƴan sandan jihar SP Odiko Mackdon ya ce an kama mutanen ne a cikin watanni uku kusa da ƙarshe na shekarar da mu ke ciki.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wata makauniya da aka kamata da ƙwarangwal ɗin kan mutane a gidanta.
Sai dai matar ta ce ba ta da masaniya a kan kawunan mutanen da aka samu a gidan nata.
Ƴan sandan sun zargi matar da haɗa hannu da masu amfani da sassan jikin mutane don wata buƙata ta daban.
Tuni rundunar ta duƙufa don zurfafa bincike a kan mutanen da aka kama sannan za su gurfanar da su a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.