Labarai
Ƴan Sanda Sun Kama Makauniya Da Ƙwarangwal Ɗin Kawunan Mutane
Rundunar ƴan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama mutane 138 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.
An kama mutanen wadnada su ka haɗa da ƴan fashi da makami garkuwa da mutane, fyaɗe da sauran miyagun ayyuka.
A yayin da yake jawabin lokacin da ya ke gabatar da masu laifin a gaban yan jarida, kakakin ƴan sandan jihar SP Odiko Mackdon ya ce an kama mutanen ne a cikin watanni uku kusa da ƙarshe na shekarar da mu ke ciki.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wata makauniya da aka kamata da ƙwarangwal ɗin kan mutane a gidanta.
Sai dai matar ta ce ba ta da masaniya a kan kawunan mutanen da aka samu a gidan nata.
Ƴan sandan sun zargi matar da haɗa hannu da masu amfani da sassan jikin mutane don wata buƙata ta daban.
Tuni rundunar ta duƙufa don zurfafa bincike a kan mutanen da aka kama sannan za su gurfanar da su a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
Labarai
Ko Gezau Zamana Daram – Martanin Ganduje Ga Gwamnatin Kano
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Ganduje ya ce sam bai girgiza ba kuma har yanzu ya na nan dara matsayin shugaban jamiyyar na ƙasa.
A wani bidiyo da ya ke yawo a kafofin sa da zumunta, Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da jam’iyyar NNPP da hannu a abinda ya kira maƙarƙashiya da aka yi masa kan batun dakatar da shi daga cikin jam’iyyar daga matakin mazaɓa.
Ganduje ya ce ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kuma ya tabbatar masa da cewar har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC.
Wannan na zuwa ne bayan da wani ɓangare na shugabancin jam’iyyar a mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawain Tofa su ka sanar da dakatar da shi daga cikin jam’iyyar.
Sai dai a wani bidiyo da aka gano shugaban jam’iyyar na mazaɓar ya ce ba da aywunsu wannan sanarwa ta fita ba, kuma waɗanda su a fitar da sanarwa ba sa tare da su.
An fara wanan sa toka sa katsin ne tun bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan Kano.
A ƴan kwanaki nan dai gwamnatin Kano ta shugar da ƙara a gaban kotu wanda take zargin tsohon gwamnan Abdullahi ganduje da yin almundahana, aiwatar da gwamnati a yadda ya kamata ba.
Labarai
Babbar Kotu A Kano Ta Tabbatar Da Dakatar Da Ganduje Daga APC
Bbbar kotun jihar Kano ta tabatar da dakatarwar da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Ganduje su ka yi wa tsohon gwamnan Kano Dakta Abdullahi umar Ganduje.
Ƙarar da Laminu Sani da Haladu Gwanjo su ka shigar gaban kotun, sun jaddada matsayarsu na dakatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ɗan jam’iyyar daga mazaɓarsa ta Ganduje.
Tun a ranar Litinin aka wayi gari da labarin wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwar jam’iyyar a mazaɓar Ganduje, das u ka sanar da dakatar da tsohon gwamnan daga cikin jam’iyar.
Sai dai daga bisani shugaban majalisar a matakin mazaɓa da shugaban majalisar na ƙaramar hukumar Dawakin Topa da ma shugabancin majalsiar a matakin jiha sun yi watsi da batun.
Jam’iyyar ta zargi mutane biyun das u ka shigar da ƙarar da cin amanar jam’iyyar, ta hanyar yi wa jam’iyyar adawa aiki kamar yadda shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar Dawakin Topa ya shaida.
A hukuncin da mai shari’a Usman Malam Na’abba ya yanke a ranar Talata, ya tabatar da matakin da mambobin biyu daga cikin tara su ka ɗauka na dakatar da Ganduje daga cikin jam’iyyar.
Bayan faruwar haka, jamiyyar APC ta zargi abokiyar hamayyarta ta NNPP da hannu a lamarin das u ka kira maƙarƙashiyar.
Sai dai tuni jam’iyyar NNPP ta nesanta kanta da hannu a ciki, wada ta ce lamari ne da ya shafi jam’iyyar APC kuma abu ne na cikin gida babu hannunsu a ciki.
Labarai
Rundunar Operation Hadarin Kai Sun Kashe Yan ISWAP Sama Da 30 A Gabar Tafkin Chadi
Rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Kai (OPHK), ta kai wani harin sama a maboyar ‘yan ta’addar ISWAP, inda ta kashe mayakansu sama da 30 a kauyen Kolleram da ke gabar tafkin Chadi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojojin saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet, ya fitar yau Talata a Abuja.
Gabkwet ya ce harin da aka kai ta sama da aka kai a ranar 13 ga Afrilu, wani mummunan hari ne na ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Ya ce aikin ya samu gagarumar nasara yayin da rundunar ‘Battle Damage Assessment (BDA)’ da ta gudanar bayan yajin aikin ta bayyana kashe ‘yan ta’adda sama da 30.
Gabkwet ya ce daga cikin wadanda aka kashe akwai wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’addan da suka hada da Ali Dawud, Bakura Fallujah, da kuma Malam Ari.
Bugu da kari, an lalata motoci da dama, babura, da kadarori, wanda hakan ya kawo cikas ga ayyukan ‘yan ta’addan.
Ya ce bayan bayanan sirri da aka tattara bayan harin ta sama suna da nasarar wadannan hare-hare ta sama na kara jaddada kudurin NAF na kawar da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaro da tsaron ‘yan Najeriya.
Ya ce wadannan hare-hare ta sama sun dace da kokarin da sojojin kasa ke yi a yankin tafkin Chadi kuma suna wakiltar wani muhimmin ci gaba a yaki da ta’addanci a Najeriya.
-
Labarai2 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata1 year ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya5 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Bidiyo4 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida