Al’ummar jihar Zamfara na ci gaba da zaman ɗar-ɗar biyo bayan ci gaba da kai hare-hare ƴan bindiga.
Mutanen da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda na ci gaba da fargaba tun lokacin da ƴan bindiga su ka ci gaba da ƙaddamar da hare-hare a ƙauyukan garin.
Sama da mutane 20 aka kashe ƙasa da mako biyu a garin kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.
Matashiya TV ta zanta da wani direba mai suna Abdullahi mazaunin Sabon Garin Ƙauran Namoda wanda ya tabbatar da cewar, a iya zirga-zirgar da yake yi kullum cikin firgici yake ganin yadda ƴan bindigan da rana tsaka ke tare hanya tare da sace ,mutane.
Abdullahi ya ce ƴan bindigan na kai harin kan manoma da ke gonaki, sannan su farwa matafiya ga wanda tsautsayi ya rutsa da shi.
Ya ƙara da cewa duk da matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka har yanzu jihar na fama da hare-hare ƴan bindiga musamman yankunan su.
An katse layukan waya a jihar Zamfara domin ɗaukar mataki a kan ƴan bindigan da su ka ɗauki tsawon lokaci su na addabar jama’a.