Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce nan gaba kaɗan Najeriya za ta kawo ƙarshen ta’ammali da miyagun ƙwayoyin a ƙasa baki ɗaya.

Shugaban hukumar a Najeriya Buba Marwa ne ya bayyana haka a yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Abuja.
Buba Marwa ya ce ƙasar na samun gagarumar nasara wajen hana fataucin miyagun kwayoyi.

Ya ƙara da cewa su na samun dukkanin goyon bayan da su ke buƙata daga gwamnatin ƙasar kuma hakan ya sa su ke samun nasara a ayyukan su.

Buba Marwa ya ce hukumar za ta fara aikin wayar da kan mutane ta hanyar shiga ƙananan hukumomi a Najeriya domin wayar da kan mutane dangane da illar shan miyagun ƙwayoyi.
A baya shugaban ya bayyana cewar akwai kaso mai yawa a Najeriya da su ke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi wanda hakan ya zamto annoba.