Shugaban mabiya mazahabar shi’a a Najeriya Sheik Ibrahim Zakzaky da matarsa Malama Zeenat sun maka gwamnatin Najeriya a gaban kotu.

Malamin da matar sa sun buƙaci gwamnatin ta biya su diyyar naira biliyan biyu a bisa ɓata musu suna da take haƙƙinsu da su k ace gwamnatin Najeriya ta yi musu.

Sun kai ƙarar gwamnatin ne domin kwace musu fasfo din su wanda hukumar ƴan sandan farin kaya su ka yi.

Babban lauyan da ke kare su Femi Falana ya tabbatar da cewar a lokaci na ƙarshe an ga fasfo ɗin nasu ne a hannun hukumar leƙen asiri ta ƙasar.

Sai dai hukumar ta musnata hakan tare da cewar fasfo ɗin nasu bay a hannun ta.

Lauyan ya ce sun yi ƙoƙarin sabunta fasfo din a hukumar shige da fice wanda su ka bayar da tabbacin cewar hukumar ƴan sandan sun dakatar da fasfo ɗin domin gudanar da bincike.

Haka kuma sun ce rike fasfo ɗin nasu babbar barazana ce ga rayuwar su domin bas u da damar fita wajen Najeriya don samun kulawa daga likitocinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: