Gwamnatin jihar Bauchi ta ware naira miliyan bakwai domin yaƙi da sauro a jihar.

Wannan ne karo na biyu da gwamnatin ta yi yunƙuri domin yaƙi da sauro don kashe sauro a wasu ɓangare na jihar.
Kuɗin da aka ware na wannan lokaci za a magance matsalar sauro a ƙananan hukumomi shida na jihar.

Daga cikin ƙananan hukumomin da za a yi amfani da kuɗaɗen don kashe sauron akwai Ningi, Katagum, Bauchi, Dass, Misau, da ƙaramar hukumar Jama’are.

Babban daranta a hukumar muhalli ta jihar Dakta Ibrahim Kabir ya shaida cewar za su yi amfani da wani sinadari wanda zai kashe sauron ba tare da ya illata dabbobi ko sauran hallittu ba.
Wannan wani mataki ne da gwamnatin ta dauka don yaƙi da ctar zazzaɓin cizon sauro wadda ta ke yaduwa a sanadin cizon sauro.