Hukumar kula da jiragen ƙasa a Najeriya NRC ta dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa a fadin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan wasu hare-hare da aka kai ta hanyar saka abubuwan fashewa a hanyar jirgin ƙasan da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja.
An kai ahrin farko a yammacin Laraba yayin da aka kai hari na biyu a ranar Alhamis da safe.

Bayan abin fashewar ya fashe an buɗewa jirgin wuta.

Hukumar ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasan kuma ba ta bayyana lokacin da za ci gaba da jigilar mutane ba.
An mayar da hankali zuwa jiragen ƙasa musamman masu zuwa Abuja daga Kaduna a sanadin matsin hare-haren ƴan bindiga da su ke kai wa a babbar hanyar mota a shekarun baya.
A makon da mu ke ciki hukumar jiragen ƙasa ta ce za a taƙaita zirga-zirgar jiragen ƙasan daga Kaduna zuwa Abuja na wasu kwanaki.