Wani jirgin ƙasa ya taka abin fashewa a yayin tafiyar sa daga Kaduna zuwa Abuja.

Jirgin ya taka abin fashewar ne a yayin da yake kan hanyar Abuja a ranar Laraba da yamma.

Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafin tuwita cewar an buɗewa jirgin wuta bayan ya taka nakiyar sai dai Allah ya tseratar da su.

Haka kuma an sake kaiw ani harin tare da saka abin fashewa a kan hanyar wani jrigin da ya nufi Abuja yau Alhamis.

Sanatan ya ce titin jirgin ya lalace a daidai wurin da aka saka abin fashewar.

Wannan ne hari mafi tsauri da aka kai tun lokacin da aka fara jigilar mutane daga Kaduna zuwa Abuja a cikin jirgin ƙasa.

Ƴan bindiga na sake dabarun kai hare-hare a daidai lokacin da ake ɗaukar matakin daƙile su a jihohi daban-daban musamman arewacin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: