Kotu a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar jagoran ƙungiyar IPOB Nnamdi Kanu na bayar da damar kai shi gidan yari maimakon ci gaba da tsare shi a wajen jami’an tsaron DSS.

Kotun ta ƙi amincewa da bukatar haka ne yayin da aka ci gaba da zaman sauraron ƙarar wadda aka yi yau a Abuja.

Kotun ta ci gaba da sauraron ƙarar da aka kai jagoran ƙungiyar IPOB da ake zargi da aikata ta’addanci wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayuwar mutane da dama musamman a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Yayin da aka kai shi kotu an tsaurara matakan tsaro tare da hana ƴan jarida ɗaukar hoton sa.

Kotun ta sake saka ranar 10 ga watan Nuwamba na gaba a matsayin ranar da za a ci gaba da shari’ar.

Gwamnatin tarayya ce ke zargin Nnamdu Kanu bisa laifuka daban-daban ciki har da goyon bayan ta’addaci da ake zargin ƴan ta’addan IPOB na kai wa wasu yankuna a kudancin ƙasar.

Tun a baya aka zargi ƙungiyar IPOB da kitsa hare-haren ta’addanci wanda har ta kai hukumar ƴan sanda ta kira su da yan ta’adda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: