Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya buƙaci gwamnatin tarayya ta buɗe layukan wayar salula a jihar.

Gwamnan na wannan jawabi ne yayin da ya karɓi baƙoncin gwamnan jihar Borno Babagana Umaara Zulum a fadarwa wanda ya je domin jajanta wa a bisa kisna mutane da dama a Goronyo ta jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar ya ce sun aikewa gwamnatin tarayya buƙatar buɗe layukan watya a jihar sakamakon hare-haren yan bindiga.

Gwamnan ya ce katse layukan wayar salula a jihar na kawo cikas wajen yaƙi da ƴan bindiga a jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an tsaro a jihar na kokawa ganin yadda ake samun cikas wajen yaƙi da yan bindigan a sanadin rufe layukan wayar.

An toshe layukan sadarwa a jihar Sokoto a wani salo da wasu jihohin Arewa su ka ɗauka na kawo ƙarshen yan bindiga baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: