Rundunar ƴan sanda a Ebonyi ta kashe wani ɗan bindiga guda ɗaya yayin da yan ta’addan su ka yi yunƙurin kai hari ofishin yan sanda.

Al’amarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe uku na dare.
A yayin da ƴan bindigan su ka kai harin, an yi musayar wuta wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayuwar wani jami’in ɗan sanda guda ɗaya.

Kakakin yan sandan jihar Loveth Odah ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce ƴan bindigan sun rufe fuskokinsu yayin da su ka kai harin.

Ta ƙara da cewar ƴan bindigan sun kai hari ofishin jami’an nasu ne ɗauke da makamai kuma yawansu sun haura talatin.
Haka kuma rundunar ta yi nasarar kwato wasu bindigu ƙirar AK47 guda biyu daga hannun su sai wasu makamai da rundunar ta kwace yayin da ta daƙile harin.
Tuni kwamishinan yan sandan jihar ya bai wa jami’an sa umarni don gudanar da bincike tare da zaƙulo waɗanda su ka kai harin.