Rundunar ƴan sanda a Katsina sun tarwatsa sansanin ƴan bindiga ƙarƙashin babban ɗan bindiga Bala Wuta.

Jami’an hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri a kan wasu sansanin yan bindiga da ke dazukan jihar.

Harin kwanton ɓaunar da dakarun su ka kai haɗin gwiwa da rundunar soji da kuma jami’an sa kai a jihar, sun kuɓutar da shanu 43 daga sansanin yan bindigan.

Sanarwar da kakakin ƴan sandan jihar Isah Gambo ya fitar ya ce akwai sauran dabbobi masu yawa waɗanda aka kubutar a sanadin harin da aka kai.

Ya ƙara da cewa an kai wani hari a dajin Ƴantumaki tare da tarwatsa sasaninsu.

Rundunar ta buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai don ganin an samar da cikakken tsaro a jihar baki ɗaya.

Wasu daga cikin jihohin Najeriya sun ɗauki matakin kawo ƙarshen ƴan bindiga ciki har da jihar Katsina wadda ke fama da hare-hare daga gare su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: