Rundunar yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta yi nasarar kuɓutar da na’ura mai kwakwalwa guda 75 waɗanda aka sace.

Kwamishinan yan sandan jihar Sunday Babaji ne ya sanar da haka a yayin da yake gabatar da masu laifin a gaban ƴan jarida.

Haka kuma akwai wasu motoci da rundunar ta kwato daga hannun ƴan fashi da kuma wadanda aka sace a wajen ajiye motoci.

Haka kuma a cikin mutanen da aka kama akwai wasu da ake zargi da kwacen motoci a babban birnin tarayya Abuja.

Akwai makamai da aka kama daga hannun masu kwacen wayar kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

Daga binciken da aka gudanar a kan masu laifin wasu sun bayyana cewar su na amfani da makullai wajen buɗe motocin da aka ajiye.

Kwamishinan ya bayyana cewar za su ci gaba da bincike a kan waɗanda aka kama kuma za a gufanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: